Wata ƙungiyar rajin kare haƙƙin yan Arewa, CNF, ta yi kira da a kama tsohon ministan sufurin jiragen sama a lokacin Buhari, Hadi Sirika tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya bisa zarginsa da zamba kan batun Nigeria Air.
Kiran na zuwa ne bayan kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama, ya bayyana batun jirgin na ‘Nigerian Air’ a matsayin zamba.
Kwamitin ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da kamfanin jirgin.
Ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis ta hannun shugabanta Ali Muhammad, ta buƙaci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), da ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama tare da gurfanar da shi gaban ƙuliya.
Muhammad ya ƙara da cewa, ministan ya yi abubuwa da dama ba tare da sauraro ko neman shawarar kowa ba. Ya ce hatta batun jirgin na Najeriya Air, bai saurari shawarar kowa ba.
“Wannan abun kunya ne da almubazzarantar da dukiyar ƙasa, wanda za a iya hana faruwarsa inda ace ya saurari shawarar masana, amma kuma Sirika ya ƙaddamar da aikin duk da sanin cewa yaudara ce kawai da aka shiryawa ‘yan Najeriya.”
Kungiyar ta kuma ce, tsawon shekaru takwas da ya yi a matsayinsa na minista, babu abin da ya yi sai zamba da kuma yaudarar ‘yan Najeriya.
A dalilin haka ne ƙungiyar ta yi kira ga Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC), da ta tuhumi Hadi Sirika bisa abin da ta kira yaudarar ‘yan Najeriya.












































