Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya ce in da jam’iyyar APC na son cigaban Najeriya da ta tsaida mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben da ya gabata.
Obi ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake ganawa da wasu baki a bikin cika shekaru 63 na Dele Momodu a birnin Landan na kasar Ingila.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, a cikin wani faifan bidiyo, ya ce yana da burin ganin Najeriya ta cigaba, inda ya kara da cewa hakan ne ya tilasta masa yin wannan takarar.
Idan dai za a iya tunawa, Bola Tinubu, na jam’iyyar APC, ya doke tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da Yemi Osinbajo inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben fidda gwani.
Daga baya ya zama zababben shugaban kasa inda ya doke Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Obi, a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Saidai Obi wanda ya shigar da karar yana kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 a kotu ya ce Najeriya na bukatar mutum mai lafiya.
Obi ya ce, “Ina matukar fatan ganin Najeriya tana aiki, ba zan iya boyewa ba. Ni ma na fuskanci su idan kuna so, me ya sa ba ku kawo Osinbajo ba domin mu samu masu son yi wa kasa aiki?













































