Dan majalisar wakilai ta tarayya Mukhtar Aliyu Betara, daya daga cikin masu neman kujerar shugaban majalisar wakilai ya ce kungiyar yan majalisar da ake kira da G-7 ne za ta yanke hukuncin wanda zai zama kakakin majalisar wakilai ta 10.
Betara ya bayyana haka ne a wajen taron da aka yi a bayyana tsayawa takara hukumance na dan majalisar wakilai kuma mamba a G-7 Ahmed Wase, a Abuja.
Ya ce kungiyarsu za ta cimma matsaya kan wanda ya dace ya jagoranci zaman majalisar a majalissar ta 10.
Betara, ya bayyana Wase a matsayin dan uwa kuma abokin aiki wanda shi ma ya cancanci shugabancin majalisar.
A cewarsa mun kafa wannan kungiya ne saboda muna adawa da tsarin da jam’iyyar ta yi na rabon shugabancin, ba fada muke yi ba kuma ba za mu yi fada ba. Muna goyon bayan dan takarar yarjejeniya.
“Za mu iya zabar dan takara daga cikin kanmu amma idan muka zauna muka yanke shawara a kai. Ina tabbatar muku da cewa mutum daya ne Allah zai zaba ya zama Kakakin Majalisa.
” Ina tabbatar muku cewa ba za mu sami wata matsala ba. Za mu amince mu goyi bayan daya daga cikin mu a matsayin kakakin majalisa,” inji shi
G-7 wata kungiya ce ta masu neman takarar shugaban majalisar dokokin kasar karo na 10, masu adawa da dan takarar da jam’iyyar APC ta tsaida.
Mambobin kungiyar sune: Betara, Wase, Sada Soli, Miriam Onuhoa, Yusuf Gagdi, Sani Jaji da Alhassan Ado-Doguwa.
A nasa bangaren, Sada Soli, akwai bukatar a yi adalci, hada kai da kuma mutunta bambancin ra’ayi wajen isa ga zabin shugaban majalisar wakilai.
Ya yi kira ga ‘yan majalisar da aka zaba da su yi kokarin kare mutunci da ‘yancin kafa majalisar.













































