Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Samaila Bagudo, wanda ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne suka sace, ya shaƙi iskar ‘yancinsa bayan shafe kwanaki a hannunsu.
Sakataren gwamnatin jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Tafida, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar daga Birnin Kebbi.
Tafida ya bayyana cewa an kubutar da ɗan majalisar ne ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro bayan shafe kwanaki a hannun masu garkuwa da mutane.
Ya ce wannan nasara ta nuna yadda gwamnatin jihar ke da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ya tabbatar da cewa Bagudo yana cikin koshin lafiya kuma yana samun cikakkiyar kulawa daga hukumomi.
Labari mai alaƙa: Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi
Tafida ya yabawa jami’an tsaro bisa irin ƙoƙarinsu wajen ceto ɗan majalisar cikin nasara, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da haɗin kai da hukumomin tsaro domin yaki da ayyukan ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a jihar.
Ya kuma roƙi jama’a su ci gaba da taimaka wa hukumomin tsaro ta hanyar bayar da bayanai da sanar da duk wani motsi da ke da hatsari a yankunansu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa an sace mataimakin kakakin ne a ranar Juma’a, 31 ga Oktoba, da misalin ƙarfe 8:20 na dare, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa garin Bagudo suka tafi da shi bayan ya idar da sallar Isha’i a hanyarsa ta komawa gida.












































