
Ƙungiyar malamai ta ƙasar Senegal mai ƙarfin faɗa a ji, ta shure tayin da shugaban ƙasar Macky Sall ya yi na yin zaben ƙasar a watan Yulin wannan shekarar.
Shugaban ya bayyana hakan ne kwana ɗaya bayan wani taron ƙasa don tattauna sabuwar ranar da za’a yi babban zabe, wanda ‘ƴan siyasa da shugabannin addini suka ƙauracewa.
“Ba mu yarda da yin zaɓe ba a duk wata ranar da ta wuce watan Afrilu. Ba ma so mu halarci taron bogi. Dole shugaban ya sake sanya wata sabuwar rana kafin biyu ga watan Afrilu. Abin da muke so ya yi kenan” kamar sakataren ƙungiyar Ismael Ndiaye, ya shaida wa BBC.
Karin labari: Babban bankin Najeriya CBN ya fara sayar da Dala ga BDC
Mafiya yawan ‘ƴan ƙasar ta Senegal musulmi ne kuma sanarwa daga ƙungiyar malaman na da babban tasiri. Shugabannin sun soki shugaba Sall da jinkirta zabe.
Lamarin da a cewarsu ya shafawa ƙasar baƙin fenti kan saninta da aka yi da ƙasa mai zaman lafiya a mulkin dimokradiyya, a yankin da ake fama da juyin mulkin soji da rashin tsaro.











































