Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa kafa kwamitocin raya yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.
Shugaban kungiyar Mamman Osuman ne ya yi wannan yabon a Gombe ranar Litinin yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Inuwa Yahaya, shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewaz har ma ya bayyana yuwuwar ci gaban tattalin arziki.
Ya bayyana cewa kwamitocin za su rage radadin talauci, rashin daidaito, da inganta ababen more rayuwa da walwala tare da inganta yanayin rayuwa ga mutane a waɗannan yankuna.
Osuman ya kwatanta kwamitocin da kamfanin ci gaban kasa na New Nigeria Ltd, wanda aka kirkira a shekarar 1949, yana mai cewa sabbin hukumomin za su bunkasa harkokin kasuwanci da masana’antu na Arewa.
Karin karatu: ACF ta yi Alkah-wadai da harin jirgin sama da aka kai a Sokoto
Ya kuma yi gargadin a guji siyasantar da nade-naden mukamai a cikin kwamitocin, tare da bukatar hadin kan gwamnatocin Arewa da ‘yan kasa don magance kalubalen yankin.
Alhaji Bashir Dalhatu, shugaban kwamitin amintattu na ACF, ya yi na’am da kiran da aka dauki mataki na bai daya har ma ya jaddada muhimmancin dawo da martabar Arewa da aka rasa.
Ya yi kira ga shugabanni da su magance wahalhalun da yankin ke ciki tare da inganta rayuwar al’ummarta.
Gwamna Inuwa Yahya ya jaddada kudirin gwamnonin Arewa 19 na tunkarar kalubalen yankin tare da yin nuni da cewa, Arewa na da wadatar albarkatun kasa domin a samu ci gaba.
Inuwa Yahaya ya bayyana cewa albarkatun yankin sun isa su biya bukatun al’ummar yankin, har ma ya yi alkawarin baiwa gwamnonin ba za su gaza wajen gudanar da ayyukansu na inganta Arewa ba. (NAN)