Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya karɓi dalibai 25 na makarantar sakandaren Maga da aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane, inda ya tabbatar da cewa dukkan su suna cikin ƙoshin lafiya bayan kubutar da su.
Gwamnan ya bayyana cewa duk labaran da suka yadu cewa an biya kuɗin fansa ba su da tushe, domin ba a biya ko sisin kobo ba wajen ceto ɗaliban daga hannun wadanda suka sace su.
Ya ce jami’an tsaro sun bi umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na tabbatar da kubutar da daliban ba tare da wata illa ta same su ba, inda dakarun sojoji da hukumar tsaron DSS suka shiga dazukan da masu garkuwa da mutane suka ɓoye.
Gwamnan ya jaddada cewa jami’an tsaro sun gudanar da aikin bincike da fatattakar ’yan bindiga ba tare da yin wata yarjejeniya ko tattaunawa da su ba, wanda hakan ya kai ga ceto daliban cikin koshin lafiya.
Labari mai alaƙa: Da ɗumi-ɗumi: Yadda ɗalibai ƴan mata 25 da aka sace a Kebbi suka shaƙi iskar ƴanci
Ya bayyana cewa rundunonin tsaro sun yi aiki tare da sauran hukumomi wajen tabbatar da an tsame ’yan matan daga hatsarin da suke ciki tun daga lokacin da aka sacen su.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa iyalan daliban tare da tabbatar da cewa suna samun kulawa ta musamman domin komawa makaranta cikin kwanciyar hankali.
Ya tabbatar wa mazauna jihar Kebbi cewa gwamnati na ƙara ƙarfafa matakan tsaro a yankuna domin kare rayuka da dukiyoyi tare da dakile hare-haren masu garkuwa da mutane a gaba.













































