Kungiyar malaman makarantun Sakandire ta kasa reshen jihar Kano ASUSS ta horar da Malaman da aka mayar aikin koyarwa 3000
Shugaban kungiyar na Jihar kano Comrade Abdu USman Yalo ya bayyana hakan a lokacin DA ake yaye malaman,
Ya ce babu shakka Gwamnatin Kano Tayi abin a yaba bisa Wannan shiri na maida wasu ma’aikata masu shaidar karatu na ilimi zuwa aikin na koyarwa,don haka suka ga dacewar basu wannan horo.
Shi ma a nasa jawabin Kwamishinan Ilimi na jihar kano wanda ya sami wakilcin Dr shehu Shu’aibu ya bayyana wannan kokari a matsayin abin a yaba bisa wannan horo da kungiyar ta bayar
Wasu malamai da suka amfana da horon sun bayyana jin dadinsu bisa wannan horo da suka samu.













































