Ƙasashen Yammacin Afirka na Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanar da janyewar su daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC), inda suka ce ba za su ƙara amincewa da ikon ta ba.
Ƙasashen da sojoji ke mulki sun zargi kotun da yin shari’a bisa son rai kan laifukan yaƙi tare da zama “makamin danniya na mulkin mallaka na zamani.”
Sun jaddada burin su na ci gaba da kare haƙƙin ɗan Adam bisa ga dabi’un su da ƙimomin su na cikin gida.
Wannan hujjar ce kuma suka yi amfani da ita a baya wajen bayyana dalilin janyewar su daga Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da kwararru na Majalisar Ɗinkin Duniya sun zargi dakarun Mali da Burkina Faso da ƙungiyoyin fararen hula masu goyon bayan su da aikata manyan laifukan yaƙi a fafatawar su da ‘yan ta’addan Islama – tare da laifukan da ‘yan bindigar suka aikata.
Hukumomin cikin gida sun ce bincike na gudana, amma har yanzu babu wani rahoto da aka bayyana ga jama’a.
Kotun ICC, wacce ke da cibiyarta a The Hague, tana hukunta manyan laifuka kamar kisan kare dangi, manyan laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama tun daga shekarar 2002.
Dukkan ƙasashen Tarayyar Turai (EU) mambobi ne, amma Amurka, Isra’ila da Rasha ba sa cikin masu rattaba hannu.
Duk da cewa suna da albarkatu masu yawa irin su zinariya da uranium waɗanda kamfanoni daga Turai da Arewacin Amurka ke hakowa inda Mali, Burkina Faso da Nijar suna daga cikin ƙasashe mafi rauni a duniya.
Ƙasashen da ke yankin Sahel a gefen kudancin Sahara suna kan manyan hanyoyin safarar mutane da kuma hanyoyin ƙaura zuwa Turai.
Tsakanin shekarar 2020 da 2023, shugabannin soji sun karɓi mulki a dukkanin waɗannan tsofaffin ƙasashen mallakar Faransa bayan gwamnatocin da aka zaɓa, waɗanda ƙasashen yamma ke goyon baya, sun kasa dakile tashe-tashen hankulan ‘yan ta’adda.
Juyin mulkin sun ƙara nisanta da abokan haɗin yamma tare da komawa wajen Rasha domin samun haɗin gwiwar soja.
NAN













































