Zanga-zangar ƴan kwangila: Majalisar wakilai za ta koma zama a ranar Laraba

HOUSE OF REPS MEMBERS 720x430

Majalisar wakilai ta tarayya za ta dawo zaman ta a ranar Laraba, sabanin yadda ta tsara a baya cewa za ta dakatar da zaman har zuwa Talata, 11 ga Nuwamba, kamar yadda sakataren majalisar, Dakta Yahaya Danzaria ya bayyana.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya tuna cewa majalisar ta dakatar da zaman ne domin ba wa shugabancinta damar tattaunawa da gwamnatin tarayya kan batun jinkirin biyan masu kwangila na cikin gida da suka kammala ayyukan gwamnati.

Masu kwangilar sun mamaye harabar majalisar tun a makon da ya gabata, inda suka hana sukunin shiga ginin majalisar ga ‘yan majalisa da ma’aikata, tare da nacewa cewa za su ci gaba da zanga-zangar har sai an biya su kuɗin ayyukansu.

Majalisar ta bai wa ministocin kuɗi, Wale Edun da na kasafi, Atiku Bagudu, wa’adin kwanaki bakwai don tabbatar da biyan masu kwangilar ayyukan da aka gudanar ƙarƙashin kasafin shekarun 2024 da 2025.

Sai dai a wata sanarwa da Danzaria ya fitar da yamma a ranar Talata, ya ce an yanke shawarar komawa zama saboda samun cigaba mai kyau kan batun biyan kuɗaɗen.

Ya bayyana cewa farkon dawowar zaman zai ba shugabancin majalisar damar sanar da mambobi cigaban da aka samu wajen warware matsalar.

Haka kuma, majalisar za ta soke matakin jinkirta zaman da ta ɗauka a baya domin ci gaba da harkokin majalisa a zaman ranar Laraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here