Yanzu-yanzu: ASUU ta yi barazanar fara yajin aiki, ta kuma bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14

ASUU ASUU NEW

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 14 domin ta magance matsalolin da ta gabatar ko kuma ta tsunduma yakin aiki.

ASUU ta ce wannan mataki ya biyo bayan taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) da aka gudanar a ranar Lahadi a Jami’ar Abuja.

Shugaban ƙasa na ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana haka a cikin wasiƙar sanarwar yajin aiki da ya sanyawa hannu, wadda ya raba wa manema labarai a ranar Litinin.

Karin labari: NELFUND ta sanar da lokacin buɗe shafin neman tallafin karatu na shekarar 2025/2026

A cikin sanarwar, kungiyar ta ce ta yi nadamar yadda gwamnati ke ci gaba da nuna halin ko-in-kula ga harkokin jami’o’i tare da ƙin cika alƙawurran da aka dade ana yi mata.

ASUU ta ce idan gwamnatin tarayya ta kasa ɗaukar mataki cikin wa’adin kwanaki 14, za ta fara da yajin aikin gargadi na mako biyu, sannan daga baya ta shiga cikakken yajin aiki ba tare da iyaka ba.

A baya gwamnatin tarayya, ta hannun ma’aikatar ilimi ta ƙasa, ta kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba sabuwar yarjejeniya da ASUU da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a jami’o’i.

Daga cikin bukatun ASUU akwai sabunta yarjejeniyar shekarar 2009 da gwamnatin tarayya, samar da kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i yadda ya kamata, biyan bashin albashi da ake bin gwamnati, da kuma samar da ingantaccen tsarin ɗaukar nauyin jami’o’i.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here