An tabbatar da mutuwar wani fitaccen ɗan fashi da makami mai suna Halifa Baba-Beru bayan wani artabu da jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano a unguwar Gwammaja da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, ya ce ‘yan sandan sun amsa kiran da aka yi musu ne da misalin karfe 1:00 na rana a ranar 22 ga Afrilu, inda aka sanar da su wani samame na fashi da makami da ake zargin Baba-Beru ya jagoranta.
SolaceBase ta rawaito cewa yan ta’addar wadanda aka ruwaito dauke da muggan makamai an ce sun addabi mazauna yankin.
A cewar sanarwar, da isar ‘yan sandan sun fuskanci turjiya mai karfi, wanda ya kai ga musayar wuta mai tsanani, daga nan ne Jami’ai biyu, Kofur Abdullahi Ibrahim da Sajan/Cadet Yahaya Saidu, suka samu raunuka a arangamar.
Tuni dai rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da cikakken bincike tare da kara zage damtse wajen cafke sauran ‘yan ta’adda masu aikata laifuka.
Kwamishinan ‘yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa za a yi adalci, har ma ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi ko kuma su bayar da bayanan da za su taimaka wajen kamo wadanda ake zargi.












































