Yan majalisar wakilai 3 daga PDP a Katsina sun koma APC

HOUSE OF REPS 750x430 (1)

Yan majalisar wakilai uku daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa (APC).

Kakakin majalisar Dakta Tajudeen Abbas ne ya karanta sanarwar sauya shekar a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Dukkan ‘yan majalisar uku sun alakanta ficewarsu da rikicin cikin gida a jam’iyyar adawa.

Abdullahi Balarabe, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Bakori/Danja, ya ce ya nemi dandali mai inganci saboda “rikicin da ya dade” a jam’iyyar PDP.

Abubakar Albaba Aliyu, wanda ke wakiltar mazabar Batasari/Safana/Dan-Musa a tarayya, ya ce ya bar PDP ne saboda “rashin hadin kai”.

Yusuf Majigiri, wanda ke wakiltar mazabar Mashi/Dutsi a tarayya, ya ba da misali da “matsalar rikicin cikin gida ba tare da magance ta ba” a cikin PDP.

Karin karatu: Ƴancin ƴan Jarida: Gwamnatin Kano ta haramta gabatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye a kafafen yada labarai

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda da shugaban jam’iyyar APC na jihar Muhammad Ali da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a jihar sun hallara a zauren taron domin shaida sauya shekar.

Majalisar dai ta ga ficewar wasu daga cikin mambobin ta a ‘yan watannin nan.

A ranar 2 ga Oktoba, 2024, Chris Nkwonta, mai wakiltar Ukwa Gabas/Ukwa ta yamma a Abia, ya bar PDP zuwa APC. A ranar 30 ga Oktoba, Sulaiman Abubakar daga Gummi/Bukkuyum a Zamfara shi ma ya koma jam’iyya mai mulki.

Ya zuwa ranar 5 ga watan Disamba, ‘yan majalisar wakilai hudu na jam’iyyar Labour da dan PDP daya sun koma APC, lamarin da ya kara karkata akalar zaman majalisar.

A ranakun 11 da 12 ga watan Fabrairu ne dai aka ci gaba da tafiyar, inda Amos Magaji daga Kaduna da Garba Koko daga Kebbi suka fice daga PDP zuwa APC.

A ranar 18 ga Maris, wasu ‘yan majalisar PDP guda biyu – Jallo Mohammed (Igabi, Kaduna) da Adamu Tanko (Gurara/Suleja/Tafa, Neja) – sun shiga jam’iyya mai mulki, saboda rikicin cikin gida na jam’iyyar.

Sama da mako guda bayan haka, a ranar 27 ga Maris, Clara Nnabuife, mai wakiltar Orumba arewa/kudu a Anambra, ta fice daga jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), tare da alakanta ficewar ta da aka yi daga harkokin jam’iyyar.

Karanta: EFCC ta kama tsohon dan majalisa Gudaji Kazaure bisa karbar Naira miliyan 70 daga hannun Emefiele

A ranar Talata ne wasu ‘yan jam’iyyar PDP shida suka koma APC, yayin da ‘yan majalisar wakilai biyu na jam’iyyar Labour Party (LP) suka koma PDP.

Obetta Chidi, mai wakiltar mazabar Nsukka/Igbo-Eze ta kudu ta Enugu, ya fice daga jam’iyyar LP zuwa PDP.

Dennis Agbo, mai wakiltar mazabar Igbo-Eze arewa/Udenu, shi ma ya fice daga LP zuwa PDP.

Victor Nwokolo, mai wakiltar mazabar Ika arewa maso gabas/Ika ta kudu a jihar Delta, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Julius Pondi, mai wakiltar mazabar tarayya ta Burutu, shi ma ya bar PDP ya koma APC.

Thomas Ereyitomi, wanda ke wakiltar mazabar Warri ta arewa/Warri ta kudu/Warri ta yamma, ya fice daga PDP zuwa APC.

Nicholas Mutu dan jam’iyyar PDP mai wakiltar Bomadi/Patani ya koma jam’iyya mai mulki, wanda tun a shekarar 1999 ya kasance a cikin majalisar.

Ukodhiko Jonathan mai wakiltar Isoko arewa/Isoko ta kudu shi ma ya fice daga PDP zuwa APC.

Ezechi Nnamdi, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Ndokwa/Ukwuani a karo na farko, ya fice daga PDP zuwa APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here