‘Yan damfara ta hanyar yanar gizo sun sace sama da N500m daga asusun wani mutum a Najeriya

4d13e005 17f6 4ab7 8093 66c7ca281a95
4d13e005 17f6 4ab7 8093 66c7ca281a95

Wasu da ake zargin cewa masu damfara ne ta hanyar yanar gizo sun wawushe naira miliyan 523,337,100, daga asusun wani kwastoma, zuwa asusuna daban-daban har goma 18.

Mai magana da yawun sashe na musamman kan ayyukan damfara na rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, SP Eyitayo Johnson, ya ce daga baya ‘yan damfarar na intanet sun aike da kudin zuwa sama da asussa 200 a bankuna daban daban.

Ya kuma kara da cewa sun yi hakan ne tsakanin ranakun 23 ga watan Afrilu zuwa 25 ga watan na Afrilu, kuma tuni sun kama mutum biyu da suke tuhuma da hannu a mummunan aikin.

BBC ta rawaitu cewa kawo yanzu an iya kwato sama da naira miliyan 160, yayin da ake ci gaba da neman mambobin wannan kungiya.

SP Eyitayo ya ce za su gurfanar da wadanda suka fara shiga hannu gaban kotu da zarar sun kammala nasu binciken.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here