Wani Mutumi da har yanzu ba’a gano cikakken bayanansa ba ya mutu a ɗakin Otal inda aka gano ya kama kuma ya shiga da wata Karuwa domin su ji daɗin juna a jihar Legas.
Jaridar Daily Trust ta rawaitu cewa Mamacin ya je Otal ɗin da ke Lagos Island tare da matar da yammacin ranar Jumu’a kuma an same shi matacce awanni bayan shigarsu.
Bayanai sun nuna cewa matar ta yi takanta daga ɗakin bayan ta fahimci cewa mutumin da suka zo tare ya mutu.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace abin al’ajabin ya auku ne a Layin Omidunu.
Yace wasu mutane sun kai rahoton Caji Ofis ɗin Adeniji Adele cewa mutumin ya je Otal ɗin da wata mace kuma sun je kwankwas masa domin sanar da shi lokacin da ya biya ya kare.
Hundeyin ya ƙara da cewa wanda ya kai ƙorafin ya faɗa wa yan sanda cewa sun buga Ƙofar dakin lokuta da dama amma shiru babu wanda ya amsa daga ciki.
Wane mataki yan sandan suka ɗauka “Bayan jin wannan rahoton nan take DPOn caji Ofis din ya haɗa tawaga ya tura su Hotel ɗin da abun ya faru. Da isarsu suka gane cewa an kulle ƙofar daga cikin ɗakin.”
“Tawagar yan sandan suka ɓalle kofar da karfin tsiya kawai suka ga gawar mutumin kwance a kan Gado kuma babu wata shaidar rikici a jikinsa.”













































