“UAE ta dage dakatarwar shiga kasarta ga ‘yan Najeriya” – Gwamnatin Tarayya

UAE, dage, dakatarwar, shiga, kasarta, 'yan Najeriya, Gwamnatin, Tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce ta cimma yarjejeniya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kan baiwa masu fasfo din Najeriya damar samun bizar tafiya zuwa wannan...

Gwamnatin tarayya ta ce ta cimma yarjejeniya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kan baiwa masu fasfo din Najeriya damar samun bizar tafiya zuwa wannan kasa ta Larabawa daga yau 15 ga watan Yuli, 2024.

Ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a ranar Litinin lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako-mako.

Karin labari: Sufeto Janar ya dakatar da aiwatar da rajistar E-CMR da aka tsara cikin watan Yuli

“Yanzu za a iya ba masu fasfo din Najeriya biza zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.”

Sanarwar ta zo ne fiye da shekaru biyu bayan da Hadaddiyar Daular Larabawa ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan Najeriya bayan da aka dauki tsawon lokaci ana takaddamar diflomasiyya da kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.

Karin labari: ’Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnoni na shirin daukar fansa

Hakan kuma na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da kamfanin jiragen sama na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Emirates Airlines ya sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya.

Kamfanin jirgin ya ce a watan Mayun da ya gabata zai ci gaba da tashi daga Legas zuwa Dubai daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2024.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here