Tsoffin ƴan sanda sun yi zanga-zanga a gaban zauren majalisar tarayya

Retired Police Officers Protest At NASS 750x430

Duk da ruwan sama da aka yi, a yau Litinin, jami’an ‘yan sanda da suka yi ritaya sun gudanar da zanga-zangar lumana a babbar kofar majalisar tarayya da ke Abuja, inda suka bukaci a cire su daga tsarin bayar da gudunmawar fansho CPS, wanda suka bayyana a matsayin cin zali da rashin adalci.

Zanga-zangar wadda aka fara a shalkwatar rundunar Louis Edet, an gano tsofaffin jami’an suna yin tattaki cikin ruwan sama mai karfi zuwa harabar majalisar dokokin kasar, suna rera wakokin haɗin kai kuma rike da takardu masu ɗauke da rubuce-rubuce irin su “Shekaru 35 na hidima, ritayar Naira Miliyan 3? Abin kunya!”, “Muna son Hukumar Fansho ta ‘Yan Sanda Yanzu!”, da “Cire ‘Yan Sanda daga CPS!”.

Retired Police Officers Protest At NASS 1 768x422

Rahotonni sun ce zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon wani faifan bidiyo na wani Sufetan ‘yan sanda mai ritaya wanda ya koka da karbar Naira miliyan 3 kacal a matsayin kudin ritaya bayan ya shafe shekaru 35 ya na aiki.

Bidiyon ya sake haifar da ƙorafe-ƙorafe da aka daɗe ana yi a tsakanin ƴan sanda da suka yi ritaya, wadanda suka ce tsarin fansho ya takaice su.

b15f4027 dc84 4efb 9bea 6d183230e916

Da yake jawabi yayin zanga-zangar, Sufeton ‘yan sanda, CSP Manir Lawal mai ritaya mai ritaya, ya bayyana shirin a matsayin cin amanar hidima da sadaukarwa ga kasa.

“Mun zo nan ne domin mu nemi gwamnati ta cire mu daga CPS, tsarin fansho na cin amana ne kuma rashin adalci,” in ji Lawal ga manema labarai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here