Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum hudu sakamakon turmutsitsin da ya faru yayin rabon zakka ta watan Ramadan a unguwar Kofar Guga a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Fabrairu, da misalin karfe 9 na dare.
Sanarwar ta ce an samu kiran gaggawa a ofishin ’yan sanda na Central Police Station da ke Katsina kan yadda jama’a da dama suka taru a gidan wani attajiri, Alhaji Dahiru Usman Sarki, da ke unguwar Kofar Guga, lamarin da ya haddasa turmutsitsi.
Ta kara da cewa, bayan samun rahoton, an tura jami’an ’yan sanda zuwa wurin domin daukar matakin gaggawa, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin kula da lafiyarsu.
Sai dai mutum hudu daga cikin wadanda suka jikkata sun rasu daga baya bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsu.
An bayyana sunayen mamatan da suka hada da Bilkisu Mamman mai shekaru 40 daga unguwar Kerau; Ihsan Musbahu mai shekaru 40 daga unguwar Abattoir; Aisha Sani mai shekaru 16 daga Kofar Sauri; da Salamatu Kabir mai shekaru 45 daga Sabuwar Unguwa.
Sauran mutum 18 sun samu raunuka mabambanta kuma ana kula da su a Babban Asibitin Katsina, yayin da wata yarinya mai shekaru 15, Hafsat Zubairu daga unguwar Masanawa, aka mayar da ita Asibitin Koyarwa na Tarayya domin karin kulawa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello Shehu, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
Ya kuma bayar da umarnin a zurfafa bincike domin daukar matakan da za su hana faruwar irin haka nan gaba.
Rundunar ta kuma bukaci duk wanda ke shirin raba tallafi ko shirya irin wannan taro da ya rika sanar da ’yan sanda tun da wuri domin samar da isasshen tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyi.













































