Zargin zuba guba ga Tinubu bidiyo ne na karya – Fadar Shugaban Kasa

President Tinubu6 750x430

Fadar Shugaban Kasa ta karyata wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ke ikirarin cewa an kama wani mai girki a Fadar Shugaban Kasa bisa zargin yunkurin ba wa Shugaba Bola Tinubu guba, tana mai bayyana labarin a matsayin kirkirarren karya.

Bidiyon, wanda ya bazu a karshen mako, ya yi zargin cewa jami’an tsaro sun cafke wani ma’aikacin dakin girki na fadar bayan samun bayanan sirri kan wasu ayyuka masu alaka da shirya abinci a wuraren da aka takaita shiga a fadar.

Haka kuma, bidiyon ya yi ikirarin cewa an tura wata runduna ta musamman ta ’yan sanda, lamarin da ya janyo kara tsaurara matakan tsaro a harabar fadar.

Rahoton da ke yawo ya kara da cewa an kama wanda ake zargin ne bayan samun barazanar tsaro mai inganci ga rayuwar shugaban kasa, inda jami’an tsaro suka fara bincike na hadin gwiwa domin tabbatar da kare shugabancin kasa.

Sai dai, Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya karyata zargin, yana mai cewa bidiyon “labarin karya ne” gaba daya kuma bai da tushe.

Ya bukaci jama’a da su rika dogaro da hanyoyin sadarwa na hukuma wajen samun sahihan bayanai, yana gargadin cewa yada rahotannin da ba a tantance ba na iya haifar da rudani da tashin hankali ba tare da dalili ba.

Zargin na zuwa ne watanni kadan bayan kama wasu sojoji bisa zargin shirin kifar da gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here