Takaddama kan zargin Emefiele da buga takardun kudi daban-daban a lokacin Buhari

zargin, Emefiele, buga, takardun, kudi, Buhari
Ana zargin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da buga kudin naira daban-daban da yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Ana zargin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da buga kudin naira daban-daban da yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

Wani tsohon darektan ayyuka na kudi a babban bankin, Ahmed Umar ya shaida a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata.

Umar ya ce dokar ta CBN ta bukaci a ba da shawarwari daga kwamitin gudanarwa zuwa ga shugaban kasa domin amincewa da nau’in zayyana da na’ura ta kowace irin kudin waje.

Karin labari: KNUPDA: ‘Yan kasuwa 5,000 za su rasa shagunansu a jihar Kano

Shaidan ya shaida wa kotun cewa fasali a cikin abinda Buhari ya amince da shi ya sha bamban da wanda Emefiele ya ba da umarnin a buga.

“Tsarin da shugaban kasa ya amince da shi yana da lambar QR, wanda kudin da ke yawo ba ya aiki. Matsayin hoton yana hannun dama, wanda CBN ya buga a hagu kuma tsarin lambar da shugaban kasa ya amince da shi ya sha bamban da wanda CBN ya samar.” Inji Umar.

Mahmoud Magaji, lauya ga Emefiele, ya yarda cewa tsohon shugaban kasar ya amince da aikin sake fasalin naira.

Karin labari: Hukumar NRC ta bayyana lokacin da jirgin kasan Kaduna zuwa Kano zai fara aiki

Ya kuma yarda cewa Buhari a ranar 29 ga watan Disamba, 2023, ya fito fili ya kaddamar da kudin naira da aka sake tsarawa a bainar jama’a domin amfani da ‘yan Najeriya a matsayin takardar kudi na doka.

Shaidan ya kuma yarda cewa kudin da aka sake zayyana yana da sa hannun (Umar) din a matsayin darakta mai kula da kudaden, inda ya kara da cewa babu wata takardar naira da za ta zama doka ba tare da sa hannun sa ba.

A ranar 15 ga watan Mayu ne dai aka gurfanar da tsohon gwamnan na CBN a gaban alkalin kotun Maryann Anenih bisa tuhumar tuhume-tuhume hudu, inda ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here