Sanata Adamu ya zargi Tinubu da yin kutse a kwamitin kolin jam’iyyar.

Tinubu Adamu
Tinubu Adamu

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Sanata Abdullahi Adamu ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Bola Tinubu da nada mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ba tare da tuntuba ko amincewar kwamitin kolin jam’iyyar APC na kasa ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Tinubu ya kaddamar da kwamiti me mutane 422 da ya kunshi jiga-jigan ‘yan siyasa da wasu fitattun ‘yan jam’iyyar da za su yi aikin fafutuka a kwamitoci daban-daban na kwamitin yakin neman zabe.

Sai dai kwanaki, bayan fitar da jerin sunayen, kwamitin kamfen din Tinubu ta dage ranar kaddamar da shi domin sauraran korafe korafe da masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar suka bukata.

Ga Cikakkiyar wasikar a kasa:

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (Jagaban Borgu)

Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC.

A madadin kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, bisa doron gaskiya da girmamawa, ra’ayi da matsayin kwamitin yakin neman zabe, dangane da batun da aka ambata a sama, a kokarin damuke ta hanyar samun gamsashiyyar makoma game da ayyuka da nauyin da ya rataya a wuyan manyan ‘yan jam’iyyar da ke da alhakin gudanar da yakin neman zabe mai zuwa.

Rubuta wannan wasika ya zama dole bisa la’akari da al’amuran da suka wakana a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, inda aka ce, an nada ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da jami’an kwamitin suka sanar cikin gaggawa, ba tare da neman amincewar kwamitin ayyuka na jamiyyar ba.

A tsawon lokacin, kwamitin ya himmatu wajen gudanar da yakin neman zabe cikin hadin kai wanda ke tattare da muradin jam’iyyar gaba daya da kuma muradin cin nasara ga yan takarkarun mu.

Dangane da wannan batu ne, kwamitin cike da mamaki da rashin jin dadi kan sanarwar manema labarai da kwamitin yakin neman shugaban kasa ya yi a ranar 23 ga Satumba, 2022, inda aka fitar da jerin sunayen wadanda aka nada da zasu jagorancin kwamitocin.

Babu shakka mai girma shugaban jam’iya, zai iya tunawa da tarurrukan da muka yi a ofishina da kuma a Sakatariyar Jam’iyyar ta kasa a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022, inda muka tattauna dalla-dalla kan yadda kwamitocin zasu kasance.

A cikin kalaman ka mai girma shugaba, ni na ke ba da damar yin tsokaci a nan kuma ni na rike da shi, ka bayyana cewa “akwai nauyi a wuyan kowa wajen samun nasarar cin zabe ga Jam’iyya da dan takara”.

Akan haka, Ina so in yi kira ga Mai Girma shugaban jamiya da ya tsaida ayyukan PCC kan yadda yake aikin shi kadai, duk da amincewa damukai na yin aiki tare da duk masu ruwa da tsaki wajen kai jam’iyyarmu ga nasara.

Da fatan za a karɓi wasikar ta wa da aminci , mai girma shugaba wassalam.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here