Sallah: Hukumar kiyaye hadɗura FRSC za ta baza jami’ai 1,889 a Kano

frsc 1

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta tura jami’ai 1,889 domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa a lokacin bukukuwan sallah karama a jihar Kano.

Kwamandan sashin, Masa’udu Matazu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin rundunar, Abdullahi Labaran, ya fitar ranar Juma’a a Kano.

Ya ce rundunar ta tura motocin daukar marasa lafiya guda biyar, motocin sintiri da sauran kayan aiki zuwa manyan hanyoyi da manyan tituna, domin saukaka zirga-zirga.

A cewar Matazu, aikin sintiri na musamman na bikin sallar zai gudana ne daga ranar 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, domin jami’au 1,348 na yau da kullum da 541 na musamman za su tabbatar da tsaro, zirga-zirgar jama’a, kula da zirga-zirgar ababen hawa, da kuma ba da kulawa cikin gaggawa ga wadanda hadarin mota ya shafa.

Karin karatu: Da ɗumi-ɗumi: Rundunar ƴan sanda ta dakatar da hawan Sallah a Kano

Yayin da yake kira ga masu ababen hawa da su mutunta dokokin hanya, Matazu ya yi gargadi game da tseren motoci da kuma tukin kananan yara a yayin bikin. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here