Sabon kwamandan hukumar kiyaye abkuwar haɗura FRSC ya kama aiki a Kano

WhatsApp Image 2025 10 09 at 10.25.13 632x430

Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano ta bayyana karɓar sabon kwamandan jiha Idris Mohammed Lawal, wanda ya kama aiki a ranar Talata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, CRC Abdullahi A. Labaran, ya fitar a ranar Laraba, inda aka bayyana cewa nadin Kwamanda Lawal ya biyo bayan ritayar wanda ya riga shi, Kwamanda MB Bature, wanda aka yaba masa bisa sadaukarwa da jajircewar da ya nuna yayin shugabancinsa.

Kafin wannan nadin, Kwamanda Lawal ya kasance shugaban ayyuka a hedikwatar yankin hukumar ta FRSC na Zone One Kaduna, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun kula da zirga-zirga da ayyukan hukumar a fadin yankin.

Hukumar ta bayyana cewa tura shi zuwa Kano na da nufin ƙarfafa tsare-tsaren kiyaye haɗura a cikin jihar.

A jawabinsa na farko bayan kama aiki, Kwamanda Lawal ya gode wa babban kwamandan hukumar da shugabancin FRSC bisa amincewa da amanar da suka ba shi, tare da jaddada kudirinsa na ci gaba da yaki da haɗurra a titunan Kano da kuma tabbatar da lafiyar masu amfani da hanyoyi.

Ya kuma bayyana muhimmancin haɗin kai, ladabi, da sauran masu ruwa da tsaki wajen cimma nasarar dogon lokaci.

Ya ce kiyaye tsaron hanyoyi aiki ne na kowa, don haka duk jami’ai da abokan hulɗa su haɗa kai wajen tabbatar da tituna masu aminci.

Jami’ai da kwamandojin hukumar a Kano sun tarbi sabon babban kwamanda da farin ciki tare da bayyana cikakken goyon bayansu gare shi a sabon jagorancin da zai fara

gudanarwa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here