Ƙungiyar ƴan Jarida NUJ reshen Jigawa ta fara rangadin a wasu kafofin yaɗa labarai don ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta aikin jarida

WhatsApp Image 2025 10 09 at 10.12.27 750x430

Ƙungiyar ƴan Jarida ta ƙasa reshen jihar Jigawa (NUJ) ta fara rangadi zuwa wasu muhimman gidajen yaɗa labarai a fadin jihar domin ƙarfafa haɗin kai da inganta alaƙar aiki tsakanin ƴan jarida da hukumomin yaɗa labarai.

Shugaban ƙungiyar, Kwamared Isma’ila Ibrahim Dutse, tare da wasu mambobin ƙungiyar ne suka jagoranci wannan rangadi, wanda ya shafi ziyartar gidajen rediyo da talabijin da ke cikin jihar.

A lokacin da suka kai ziyara ga gidan talabijin na Najeriya (NTA) Dutse, Kwamared Dutse ya yabawa tashar bisa ingancin shirye-shiryenta da labaranta, wanda ya ce suna taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban jihar Jigawa.

Ya kuma jaddada cewa ƙungiyar NUJ za ta ci gaba da tabbatar da cewa muryar jama’ar Jigawa tana da wakilci a cikin labaran da ake yada wa.

Karin labari: kungiyar `yan jarida ta kasa, NUJ, ta musanta zargin tsawaita wa`adin mulki

A nasa jawabin, babban manajan NTA Dutse, Malam Ibrahim Muhammad, ya godewa shugabancin NUJ bisa ƙoƙarin farfaɗo da martabar aikin jarida a jihar da ƙasa baki ɗaya, tare da tabbatar wa ƙungiyar da goyon bayan tashar.

Ƙungiyar ta kuma ziyarci Freedom Radio Dutse, inda manajan tashar, Alhaji Ali Aminu Falaki, ya yaba da yadda NUJ ke ƙarfafa ɗa’a da ƙwarewa a aikin jarida, yana mai cewa irin wannan ziyara na ƙara karfin gwiwa da haɗin kai a tsakanin ƴan jarida.

Haka kuma, tawagar ta kai ziyara ga Gidan Rediyon Jigawa, inda babban darakta, Alhaji Yusuf Adamu Babura, ya sha alwashin ci gaba da haɗin kai da NUJ wajen kare muradun ƴan jarida da kuma jama’ar jihar Jigawa.

A tashar Talabijin ta Jihar Jigawa (JTV), babban darakta Alhaji Abba Tukur, ya tarbi tawagar NUJ da farin ciki, yana mai bayyana ziyarar a matsayin mataki mai mahimmanci wajen gina kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin tashar da ƙungiyar ƴan jarida ta jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here