Sabon farashin kuɗin fasfo a Najeriya ya tayar da cece-kuce

E Passport

Al’ummar Najeriya sun nuna damuwa kan karin kuɗin fasfo da gwamnatin tarayya ta ƙara da kashi 100, wanda ya fara aiki daga p1 ga Satumba.

Sabon tsarin ya tanadi cewa a Najeriya, fasfo na shafi 32 da shekaru 5 zai koma Naira 100,000, yayin da na shafi 64 da shekaru 10 zai kasance Naira 200,000. Amma a ƙasashen waje, kuɗin ya rage yadda yake, zuwa Dala 150 da $ Dala 230.

Yawancin ’yan ƙasa sun koka cewa sabon kuɗin ya yi tsada fiye da karfin talakawa, musamman matasa da ɗalibai da ke neman karatu a waje. Wasu mata ’yan kasuwa da ɗalibai sun bayyana cewa karin zai iya hana su cika burinsu na tafiya kasashen waje ko samun damar karatu.

Sai dai wasu masu hulɗa da harkokin tafiye-tafiye sun ce karin bai zama abin mamaki ba, tunda tsarin fasfo na zamani da tsaro sai an kashe kuɗi. Sun bukaci gwamnati ta tabbatar da cewa sabon tsarin ya kawo sauƙi, ba tare da jinkiri, cin hanci ko biyan kuɗin da ba a rubuta ba.

Karanta: Hajjin 2026: Kano ta sanya Naira Miliyan 8.5m a matsayin kuɗin ajiya, daidai lokacin da NAHCON ta baiwa jihar kujeru 5,684

Wasu ’yan ƙasa sun ce abin da ya fi damun su ba kuɗin ba ne, illa dai jinkirin karɓar fasfo da tilastawa mutane su dawo sau da dama. Sun bukaci a samar da tsari da zai bada tabbacin samun fasfo cikin lokaci ƙanƙani.

A martanin gwamnati, Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce an kafa sabbin gyare-gyare da za su tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya zai samu fasfo ɗinsa cikin mako guda bayan rajista. Ya kuma ce an kafa cibiyar buga fasfo da za ta tabbatar da saurin aiki da hana cin hanci.

Ministan ya tabbatar da cewa ba za a bar jami’an hukumar su riƙa jinkirta ko amincewa da aikace-aikacen fasfo ba, domin an mayar da tsarin zuwa na kai tsaye don kawar da rashawa da matsalolin da ake ta fama da su a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here