Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi zai yi zaman tattaunawa da shugabannin addinai a yankin Kaduna ta Kudu, kana zai ziyarci sarakuna a yankin.
Hakazalika, Obi zai gudanar da wani taron gangami a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, inda zai gana da dalibai daga makatrantu daban-daban da kuma ‘yan a mutun jam’iyyar da magoya bayansa.
Wannan na fitowa ne daga bakin kakakin jam’iyyar, Dr Yunusa Tanko a yayin wata gwarya-gwaryar zama a jihar Kaduna.
Ya kuma bayyana cewa, Obi zai kai ziyara zuwa fadar Sarkin Zazzau, Amb, Ahmad Nuhu Bamalli da kuma Sarkin Jema’a a Kafancan da ke yankin Kudancin jihar.
Dr Tanko ya kuma bayyana cewa, a yayin taron na kamfen, Obi zai karanto manufofinsa bakwai da yake son cimmawa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben bana.
Peter Obi na ci gaba da tallata kansa da manufofinsa ga ‘yan Najeriya, hakazalika, yakan fadi maganganu da nuna nagarta da kwarewarsa a mulki.













































