El-Rufai bai isa ya sa mu bar PDP ba – Sule Lamido

65325cd0 021a 11f0 a3d3 5f4a250d1ad4.jpg

Tsohon gwamnan Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP Alhaji Sule Lamido ya yi wa tsohon gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai raddi kan tayin da ya yi wa ƴansiyasa su bi shi zuwa sabuwar jam’iyyarsa ta SDP.

A makon da ya gabata ne Malam Nasir El-Rufai ya sanar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta APC zuwa SDP.

A hirarsa ta musamman da BBC bayan ficewarsa APC, Malam Nasir El-Rufai duk da cewa bai ambaci sunan Sule Lamido ba amma ya yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban ƙasa da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola da ma dukkan shugabannin adawa su bi shi zuwa sabuwar Jam’iyyarsa ta SDP.

Sai dai Alhaji Sule Lamido tsohon gwamnan jihar Jigawa ya yi kakkausan suka kan tayin na Malam Nasir El-Rufa’i inda yake nuna cewa ba shi da akidar siyasar ci gaba da kishin al’umma da har zai yi kira ga ‘yan PDP su bi shi sabuwar jam’iyyarsa.

Karin karatu: A Daina yi wa masu yiwa ƙasa hidima barazana don sun soki gwamnatin Tinubu – Amnesty International ta gargadi NYSC

“Yanzu ba don raini ba, saboda Allah, ya zai kalle mu a PDP ya ce zai kira mu wata jam’iyyar siyasa. Jam’iyyar da muka yi ta PDP ita ce ta haife shi.”

“Ya za a yi a ce jika ya ce kakansa bai san komi ba,” in ji Sule Lamido.

A cikin martaninsa, Sule Lamido ya ce El-Rufai ya taɓa cewa babu manya a Najeriya a siyasa, su ne manya don saboda a lokacin yana gwamna. Su ne masu aiki da iko ta ko’ina.

“Amma ya wayi gari ya ce ya fadawa Buhari, Yanzu ai ba za ka kalle ni ka ce na bi umarnin Buhari ba, idan dai har haka ne bai kamata ya je wajen Buhari ba tun da ya ce su ne manya,” in ji Sule Lamido.

Sule Lamido wanda ya ce ya taba sakataren jam’iyyar SDP, ya ce shi bai ga laifin jam’iyyarsa ta PDP ba a yanzu.

“Duk rikicin da PDP take ciki, a nan aka haife shi. Idan ya ce PDP ta mutu to a nan ne asalinsa, nan ne aka haife shi.”

“Za a ce El-Rufai ministan PDP ne, duk bin da ka mallaka duniya PDP ce,” a cewar Sule Lamido

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here