Mohammed Bara’u ya karbi mukamin ne a matsayin sabon kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kan jama’a Abdullahi Labaran ya fitar ranar Litinin a Kano.
Labaran ya ce Bara’u ya karbi ragamar aiki ne daga hannun kwamandan sashen da ya bar aiki, Masa’udu Matazu, biyo bayan sake tura manyan kwamandoji da aka yi a fadin kasar baki daya a kan wasu dokokin FRSC.
A cewarsa, sabon kwamandan ya fara aiki a hukumance a ranar Litinin bayan da ya samu nasara a matsayin shugaban gudanarwa na shiyyar, hedikwatar FRSC shiyya ta daya, Kaduna.
Karanta: Tinubu zai gana da kamfanonin samar da lantarki kan bashin tiriliyan huɗu – Minista
Ya ce sabon kwamandan zai kawo nuna gogewa da kuma himma mai ƙarfi ga aikin hukumar na inganta amfani da hanyoyi a Najeriya.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano da masu ruwa da tsaki da sauran jama’a da su bayar da hadin kai ga hukumar FRSC domin inganta hanyoyin kiyaye hadurra da rage hadurran ababen hawa a fadin jihar.(NAN)