Bashir Tofa: Mun yi rashin dan kasa- Gamayyar Kungiyoyin Arewa

D720A55E 7C8B 415B A62D 93A9F9D08C3D
D720A55E 7C8B 415B A62D 93A9F9D08C3D

Gamayyar Kungiyoyin Arewa, a  yau Litinin  ta bayyana alhininta game da rasuwar dan siyasar Kano kuma tsohon dan takarar jam’iyyar Republican a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, Alhaji Bashir Othman Tofa, inda ta bayyana shi a matsayin “babban jigo kuma jagora. ”

Kungiyar ta CNG a cikin sakon ta’aziyyar da ta fito daga mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, ta ce tana matukar godiya ga marigayi Bashir Tofa wanda yayi jagoranci, sadaukarwa, da kishin kasa tare da jajircewa wajen ganin  ga al’ummar Arewacin Najeriya da ‘yan Nijeriya gaba daya sun samu shugabanci mai kyau wanda zai kawo ci gaba.

Sanarwar ta ce, “Muna jimamin rasuwar wannan mutumi mai girma wanda muka samu kwarin gwiwa a rayuwarsa da ayyukansa kuma dole ne mu yi kokari, a duk abin da muke yi, mu rayu bisa ka’ida da dabi’u na rayuwa da zamantakewa kamar yadda marigayi Bashir Tofa yayi.

Lallai Arewa ta yi asarar babban jigo,  matasan sun rasa jagora, masanin tarihin rayuwa sannan kuma yana da  kyawawan halaye da ya kamata matasan Arewa su yi kokarin cimmawa.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya gafarta masa tausasawa, ya shigar da shi Aljanna, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin,” in ji CNG.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here