Kwara: Ƴan ta’adda sun kai mana hari na fiye da sa’o’i 10 kafin sojoji su iso – shugaban ƙauyen Woro

Bandits 695x430

Shugaban al’ummar Woro a jihar Kwara, Umar Bio Salihu, ya bayyana cewa ’yan bindiga sun yi ta kai hari a yankin na tsawon kusan sa’o’i 10 kafin jami’an tsaro su iso, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da lalata wasu ƙauyuka.

Salihu ya bayyana hakan ne a wani shiri na tashar talabijin na ARISE a ranar Alhamis, inda ya ce maharan sun fara kai farmaki tun misalin ƙarfe biyar na yamma, amma sojoji sun iso ne da misalin ƙarfe uku na asuba a washegari, bayan ’yan ta’addan sun riga sun fice daga yankin.

Ya ƙara da cewa a lokacin harin babu wani farmakin sama da aka kai, tare da bayyana cewa jami’an soji ba su yi artabu da maharan ba saboda sun iso ne bayan an kammala hare-haren.

Shugaban ƙauyen ya ce al’ummar sun shiga cikin haɗari ne bayan da aka janye sojojin da ke sansanin da ke yankin, bayan wani hari da aka kai musu a baya.

Ya ce tun watanni uku zuwa biyar da suka wuce, bayan an kai hari kan sojojin da ke sansanin, aka kwashe su gaba ɗaya, lamarin da ya bar yankin ba tare da wata kariyar tsaro ba.

Ya bayyana cewa wannan yanayi ne ya bai wa ’yan ta’addan damar shiga yankin a kowane lokaci su aikata abin da suka ga dama.

Labari mai alaƙa: Harin ƴan ta’adda: An yi jana’izar bai ɗaya ga gawarwaki 78 a Kwara

Ya kuma ce maharan na cikin ƙungiyar ta’addanci ta Mamuda, kuma harin ya biyo bayan ƙin amincewar al’ummar yankin da akidar ƙungiyar.

Salihu ya yi watsi da ikirarin cewa kisan yana da alaƙa da addini, inda ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda aka kashe Musulmi ne.

Ya ce kusan kashi 95 cikin ɗari na Musulmi ne, yayin da kashi biyar cikin ɗari Kiristoci ne.

Ya kuma ce tun da farko ya kai rahoton wata wasiƙar barazana da ake zargin ’yan ta’addan sun aika zuwa ga hukumomin tsaro, amma yana zargin bayanan sun samu tangarda a lokacin da aka riƙa musayar su tsakanin hukumomi.

Ya ƙara da cewa bayan samun wasiƙar, jami’an tsaro sun yi sintiri, wanda hakan ya fusata ’yan ta’addan.

Shugaban ƙauyen ya ce an riga an binne aƙalla mutane 75, amma adadin na iya ƙaruwa saboda ana ci gaba da gano gawarwaki a cikin daji.

Ya ƙara da cewa ƙauyuka da dama sun ƙone gaba ɗaya a harin, ciki har da gidansa.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ziyarci yankin tare da bayar da umarnin tura jami’an tsaro, yayin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da tura bataliyar sojoji domin dawo da tsaro a yankunan da abin ya shafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here