Kogi: Kotu ta kure karar da Adeyemi ya shigar gabanta yana mai kalubalantar zabben fitar da gwanin da ya bawa Ododo Nasara a APC

Smart Adeyemi  750x430
Smart Adeyemi 750x430

Babbar kotun tarayya dake zamanta a abuja, a ranar Laraba ta kure karar da mai neman tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar APC, Smart Adeyemi ya shigar gabanta yana mai kalubalantar zaben fittar da gwanin da Usman Ododo yai nasara, a karkashin tutar Jam’iyyar APC.

Karar mai lamba ta FHC/CS/556/2023 wacce Smart Adeyemi ya shigar, ya nemi kotun data suke zaben fitar da gwanin da APC tayi, wanda Usman Ododo ya lashe zaben, wanda kuma shine dan takarar gwamna na APC a zaben gwamnan da za’ayi a watan Nuwamba mai zuwa.

A cikin karar da ya shigar, Smart Adeyemi ya bayyana zaben a matsayin wanda ba hallar tattce ba, kuma ya sabawa sashi na 177 na kudin tsarin milkin kasar nan.

Ya kuma nemi kotun da ta bawa hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa INCE umarni ta zare sunan Usman Ododo daga cikin wanda zasu shiga zaben gwamnoni na jihar ta Kogi.

Ya yin da yake yanke wukunci, mai shara’a James Omotosho ya ce karar da aka shigar bata da wata makama, inda ya kara da cewa wadan da suka suka shigar da kara sun yi zarge zarge da dama wadan da kuma suka kasa kawo hojjojin da zasu tabbatar da zargin sa gaskiya ne.

Inda a karshe mai shara’ar ya yi batali da karar, bisa rashin gamsassun hojjoji.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here