Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Hukumar tsara harkokin ilimi da gudanarwa ta Najeriya (NIEPA-NIGERIA), ta nuna damuwarta kan yadda Kashi 70 cikin ɗari na yara a Najeriya ba sa iya karatu da lissafi mai sauƙi, kamar yadda wani rahoto ya nuna.
Bayanin wani ɓangare ne na binciken da aka yi kan nasara ko cigaban koyo a Najeriya, wanda ya fito da irin matsalolin da tsarin ilimi yake da su a ƙasar.
Karin labari: Babbar Kotu a Kano ta magantu kan shari’ar Ganduje da matarsa da wasu mutum 6
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa shugaban hukumar, Dakta David Shofoyeke, ne ya nuna damuwar a lokacin yayin buɗe wani taron karawa juna sani na malamai da manyan jami’an kula da ilimi da shugabannin makarantu, na jihohin arewa maso yamma, kan tafiyar da harkokin makarantu a ƙarni na 21.
Shugaban ya kuma lura cewa kashi 49 cikin ɗari ne kawai na yara da ke zuwa makaranta suke iya karatu da kuma fahimtar abin da suka karanta.
A ɓangaren lissafi kuma ya ce, kashi 55 cikin ɗari ne kawai ke iya lissafi mai sauƙi.