Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya TCN yace ya gyara wutar lantarki bayan da ta katse a ranar litinin.
Wutar lantarkin ta katse tun da misalin karfe 1 da mintuna 49 na ranar litinin din 11 ga watan Disambar 2023.

Karanta Wannan:Tinubu ya kaddamar da Motoci masu amfani da wutar lantarki kashin farko a Maiduguri
A wata sanarwa da Janar manaja kan harkokin jama’a ta kamfanin Ndidi Mbah, ta fitar da yammacin litinin, tace TCN ya gyara wutar a mafiya yawan sassan kasar ban da yankin Jos.
Sai dai a lokacin da ta fitar da wannan sanarwar tace nan da sa’a guda ana sa ran za a gyara wutar a yankin Jos.












































