Gidan rediyon Andalus mai magana da yawun al-Shabab ya rawaito a yau cewa waɗanda suka mutu a harin da jirgin mara matuki ya kai sun haɗa da yara bakwai da mata shida.
“Jiragen marasa matuka mallakin gwamnatin Turkiyya sun fara harba makami mai linzami a wani masallaci a ƙauyen Bagadaza, inda mutane ke sallar Taraweeh sallar dare na musamman da aka yi a cikin watan Ramadan.
Karin labari: Za’a sake tattaunawar neman tsagaita wuta a Gaza
Bayan haka, waɗanda suka tsira daga harin na ƙokarin tserewa zuwa ƙauyen ne aka sake harbo su da makami mai linzami na biyu,” in ji Rediyon Andalus.
Al-Shabab ta ƙara da cewa mutane 12 kuma sun jikkata a harin da aka kai ta sama.
Kawo yanzu dai babu wani tabbaci kan wannan ƙazamin harin da ake zargin an kai.