Jami’an hukumar kula da shige da fice suk kwace fasfo ɗin Sanata Natasha a filin jirgi

WhatsApp Image 2025 11 04 at 8.37.14 AM 472x536 1 472x430

An samu hayaniya a filin jirgin sama da safiyar yau Talata, bayan da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya ta zargi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da bayar da umarnin a kwace mata fasfo domin hana ta tafiya ƙasashen waje.

A cikin wani faifan bidiyo da ta yada kai tsaye daga filin jirgin, an ga sanatar tana nuna bacin ranta yayin da jami’an hukumar kula da shige da fice suka riƙe mata fasfo fiye da mintuna ashirin, tana tambayar dalilin hana ta tafiya.

Sanatar ta bayyana cewa ba wannan ne karon farko ake yi mata irin wannan abin ba, tana mai cewa a baya ma sai da wani mutum mai tasiri ya shiga tsakani kafin aka dawo mata da fasfo ɗinta.

Ta kuma jaddada cewa babu wani umarnin kotu da ya ba da damar riƙe mata fasfo, tare da bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya riga ya umarci shugaban majalisar dattawa da a dakatar da duk wasu shari’o’in siyasa da ake yi mata.

Natasha ta ce tana zuwa kotu duk lokacin da ake kira, kuma ba ta da wani haɗari ga ƙasa, tana tambayar dalilin da ya sa ake yi mata kallon kamar mai laifi.

Bayan da ta dade tana takaddama da jami’an, daga bisani wani jami’in shige da fice ya dawo mata da fasfo ɗinta. Duk da haka, har yanzu babu wata sanarwa daga ofishin shugaban majalisar dattawa ko hukumar shige da fice ta ƙasa kan lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here