Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, tare da shugabannin manyan makarantu da sauran masu ruwa da tsaki, sun sanya mafi karancin maki na shekarar 2024 zuwa 2025 na samun gurbin karatu a manyan makarantun Najeriya a matsayin 150.
A taron manufofin JAMB na shekarar 2025 da aka yi yau Talata a Abuja, masu ruwa da tsakin sun amince cewa mafi karancin maki 150 na shiga jami’o’in Najeriya zai kasance, yayin da kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi za su dauki dalibai daga matakin farko idan suna da maki 100.
Ga kwalejojin kimiyyar jinya, an sanya mafi ƙarancin maki a kan 140.
Taron wanda Ministan Ilimi, Maruf Alausa ya jagoranta, ya samu halartar shugabannin jami’o’i da na makarantun gaba da Sakandare da shugabannin hukumomin gudanarwa.
Shugaban hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya jaddada cewa makin da aka amince da su shi ne mafi karanci kuma babu wata makaranta da aka amince ta ɗauki ɗaliban da ke da ƙasa da su.
Haka kuma ya ce, manufar yin hakan ita ce tabbatar da gaskiya da samun dama da inganci a cikin hukumar.
Taron manufofin ya kuma sake tabbatar da kasancewar ci gaban cin gashin kai na hukumomi a da kuma tabbatar da nagartar fannin.
Ana sa ran cibiyoyi za su kammala shirye-shiryensu na shiga jami’o’i kamar yadda aka amince da su sannan su gabatar da rahoto ga JAMB domin gudanar da ayyukansu.
Hukumar ta bayyana cewa; “An kayyade mafi karancin makin da za a iya shiga karatu na gaba a kan 150 na jami’o’i, 100 na Kwalejojin Fasaha 100 na kwalejojin ilimi da 140 sai na kwalejojin ilimin jinya da masu ruwa da tsaki.”













































