ACRESAL ya fara koyar da ilimin sauyin yanayi a makarantun Kano

WhatsApp Image 2025 07 08 at 14.54.26 1 750x430

A wani ɓangare na mataki na biyu na shirinta sauyin yanayi na CCE, shirin kula da harkokin noma a wuraren da ke fama da matsalolin sauyin yanayi watau ACReSAL ya gudanar da wani gangamin wayar da kan jama’a a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta ‘Yan Mata da ke Kano a karkashin shirin “Catch Them Young” da ke da nufin raya ilmantar da matasa musamman ta fuskar karewa da kuma bunƙasa dorewar muhalli.

Wata sanarwa da jami’ar sadarwa ta shirin na ACReSAL, Maryam Abdulkadir ta fitar a ranar Litinin, ta ce shirin na neman bai wa dalibai ilimi da kayan aiki na don tunkarar kalubalen da suka shafi yanayi tun suna kanana.

A cewar sanarwar, mukaddashin shugaban shirin na ACReSAL na Kano Dakta Abdulhamid Bala, a nasa jawabin, ya bayyana illolin da sauyin yanayi ke ci gaba da haifarwa, wanda ke ci gaba da yin babbar barazana ga dorewar muhalli a duniya.

Ya jaddada cewa waɗannan ƙalubalen suna buƙatar ayyuka na dabaru da gaggawa.

Abdulhamid ya jaddada mayar da hankali kan aikin ga ɗalibai a matsayin masu kawo sauyi, inda ya bayyana cewa ACReSAL ya himmatu wajen cusa ingantattun ayyukan muhalli a zukatan matasa ta hanyar shirinta na “Catch Them Young”.

Daga nan ya bukaci daliban da su zama jakadun muhalli na jihar Kano ta hanyar wayar da kai  a duk inda suka tsinci kansu.

SolaceBase ta ruwaito cewa yayin gudanar da shirin, ACReSAL ya haɗa ƙwararrun masana muhalli da masana kimiyya da ƙungiyar aikin don sauƙaƙe zaman tattaunawa kan ilimin kan sauyin yanayi.

Dakta Ummi Khaltum Muhammad daga cibiyar nazarin aikin noman a wuraren tsandauri ta Jami’ar Bayero da ke Kano, da Farfesa Muhammad Alhaji daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano KUST Wudil, sun jagoranci wata tattaunawa mai gamsarwa da dalibai kan musabbabi, tasiri da kuma dabarun magance matsalolin sauyin yanayi.

A wani bangare na shirin, an ware ingantattun ƴaƴan itatuwa guda 100 ga makarantar domin yin dashe saboda bunkasa ci gabanta.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here