Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya 144 da suka makale daga Yamai a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar ta karbi mutanen ne a ranar Litinin.
Dr Nuradeen Abdullahi, babban jami’i a hukumar ta NEMA na shiyyar Kano ne ya tarbi mutanen da suka dawo a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da ke birnin Kano.
Abdullahi wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar NEMA Kano, Malam Suleiman Sa’ad-Abubakar, ya ce, wadanda suka dawo sun iso filin jirgin ne da misalin karfe 2:30 na rana.
“Kamfanin SKY MALI Airlines ne ya kwaso wadanda suka dawo Najeriya da kamfanin jirgin Ethiopia B737-400 mai lamba UR-CQX”
Ya ce an dawo da mutanen ne karkashin kulawar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa IOM daga Yamai ta hanyar shirin mayar da su gida bisa son ransu.
“Shirin na mabukata ne, wadanda suka bar kasar don yin sana’o’i a kasashen Turai daban-daban kuma ba su iya komawa gida ba sakamakon tangardar da suka samu yayin tafiyar,” in ji shi.
Ya ce, wadanda suka dawo sun hada da manyan maza 106, da manyan mata 16 da yara 22 da suka kunshi mata 10 da maza 12.
Abdullahi ya lura cewa wadanda suka dawo sun fito ne daga Kano da Kaduna da Katsina da Abia sai Sokoto da Edo da dai sauransu.
Ya ce, wadanda suka dawo za su samu horo kan sana’o’i daban-daban.
“Shawarata ga ’yan Najeriya ita ce su guji jefa rayuwarsu cikin hadari ta hanyar tafiye-tafiyen ci-rani a kasashen ketare.












































