Hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta sanar da cewa za ta fara atisayen horas da rukunin Na na 2025 Batch “B” Stream II wanda zai fara ne a duk faɗin ƙasar nan daga ranar Laraba, 24 ga Satumba, 2025 a sansanonin horaswa na ƙasa.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Internet a ranar Litinin, an bayyana cewa yin rajista zai ci gaba har zuwa ƙarshen daren Juma’a, 26 ga Satumba, yayin da za a gudanar da bikin rantsuwar shiga aikin ƙasa a wannan rana.
Atisayen horarwar na makonni uku kuma zai ƙare da bikin rufewa a ranar Talata, 14 ga Oktoba, 2025.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa a Jihar Kwara, atisayen horarwar zai fara ne daga Talata, 30 ga Satumba zuwa Litinin, 20 ga Oktoba, 2025.
Darakta-Janar na hukumar, Birgediya-Janar Olakunle Nafiu, ya bukaci dukkan masu shirin shiga aikin da su je sansanonin da aka nuna a cikin takardun kiran shiga, tare da bin dukkan ka’idojin rajista.
Ya gargadi masu shirin shiga aikin ƙasa da su guji amfani da takardun bogi, inda ya ce duk wanda aka kama da hakan za a mika shi ga hukumomin tsaro don gurfanar da shi.
Haka kuma ya umarci waɗanda suka kammala kwalejin da ke koyar da fanni ɗaya “monotechnic” da kwalejin fasaha da su gabatar da takardun shaidar samun difloma na ƙasa yayin rajista.
Karin labari: Hukumar NYSC ta sanar da sabuwar ranar da za ta fara biyan alawus na Naira dubu 77
Hukumar ta kuma shawarci sabbin jami’an hidimar ƙasa da su guji yin tafiye-tafiye da dare.
Ta ce idan lokaci ya kai ƙarfe shida na yamma, ya dace su tsaya a sansanonin sojoji ko na ‘yan sanda, ko kuma a ofisoshin hukumar mafi kusa, don guje wa fadawa hannun miyagu.
Haka nan hukumar ta ja hankalin masu shirin shiga aikin ƙasa da su yi amfani da tashoshin mota da gwamnati ta amince da su ko kamfanonin sufuri na gaskiya, don kauce wa fadawa cikin haɗarin masu aikata laifi.
Darakta-Janar na hukumar ya kuma bayyana cewa duk wanda ya ƙi shiga aikin ƙasa ko kuma ya shiga ba bisa ƙa’ida ba za a gurfanar da shi a gaban kotu, bisa tanadin dokar hukumar.
Ya ƙara da cewa matan aure, masu juna biyu da masu shayarwa da aka tura wajen jihohin mazajensu za su iya kammala atisayen a jihohin da suke zama idan sun gabatar da hujjar aure, katin mazajensu da kuma shaidar zama.
A ƙarshe ya jaddada cewa dukkan mahalarta dole ne su gabatar da takardun kiran shiga na asali, sakamakon karatu ko shaidar kammala karatu, katin ɗalibai, da takardar shaidar lafiya daga asibitin gwamnati ko na soja da Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya ta amince da ita.
Haka kuma likitoci da sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya dole su nuna shaidar rajista da ƙungiyoyin aikinsu.













































