Harin Sojin Sama ya hallaka ƴan bindiga da dama a Neja

NAF airstrikes

Dakarun Operation Fansan Yamma na Rundunar sojin saman Najeriya NAF, sun ƙaddamar da hare-hare ta sama inda ta kashe ƴan ta’adda da dama a jihar Neja, tare da tallafawar sojojin kasa da ke kai hare-hare a baya-bayan nan.

Ayyukan, wanda aka aiwatar tsakanin ranakun 24 zuwa 26 ga watan Yunin bana, an gudanar da su ne bayan samun ingantattun bayanan sirri, a cewar sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a da yada labarai na rundunar Sojin Saman Air Commodore Ehimen Ejodame, ya fitar yau Juma’a a Abuja.

Ya ce dakarun rundunar sojin saman ta hanyar hadin gwiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin, ta gano ayyukan ta’addanci da suka hada da hare-hare da satar shanu a yankunan Kakihun da Kumbashi.

“Aikin ya nuna kwarewar dakarun Sojin saman bisa saurin mayar da martani, da kuma haɗa kai da sojojin kasa da sauran hukumomi.

“Rundunar sojin saman ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya baki daya tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a fadin kasar,” in ji shi.

Rundunar Sojan Sama ta aiwatar da kai hare-hare da dama wanda ya kawar da dimbin ‘yan ta’adda tare da lalata kayan aikinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here