Gwamnatin Kwara ta tabbatar da kashe gawurtaccen shugaban gungun masu garkuwa da mutane Maidawa ta hanyar amfani da jiragen yakin NAF

NAF NAF

Gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da cewa an kashe shugaban wata gungun masu garkuwa da mutane da ake kira Maidawa tare da wasu daga cikin yaransa a hare-haren jiragen saman rundunar sojin sama ta Najeriya da ake gudanarwa a dazukan Isanlu-Isin da makwabtansu a jihar Kogi.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Rafiu Ajakaiye, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce bayanan da aka samu daga tattaunawar ’yan bindiga sun tabbatar da cewa an kashe Maidawa da wasu daga cikin mabiyansa a artabun da jami’an tsaro suka yi da su a dajin Isanlu-Isin, a jihar Kwara.

Sanarwar ta kara da cewa wannan arangama ta faru ne a ranar 30 ga Satumba yayin da dakarun tsaro ke ci gaba da kai farmaki don kawar da miyagun ’yan ta’adda daga yankin, kamar yadda hukumar tsaron cikin gida ta shaida.

Har ila yau, sanarwar ta ce wani fitaccen dan garkuwa da ake nema ruwa a jallo mai suna Baccujo ne ya sanar da mutuwar Maidawa ga sauran abokan harkallarsa a hanyarsu ta Igboro-Idofin, inda ya tattauna da wasu daga cikinsu da ke Marabar Maigora, karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Karanta: Lugudan wuta ya yi sanadiyar mutuwar akalla mayakan ISWAP 70-NAF

Gwamnatin jihar ta ce sakamakon wannan ci gaban, jami’an tsaro sun kara kaimi wajen kawar da barayin da suka dade suna kai hare-hare kan al’umma tare da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

Hare-haren jiragen yakin na NAF da sauran dakarun tsaro za su ci gaba da karkata zuwa dukkan yankunan da aka yi garkuwa ko hare-hare a ’yan makonnin nan ciki har da Ekiti, Ifelodun, Isin, Edu da Patigi. Wannan ya biyo bayan mummunan harin da ’yan ta’addan suka kai a garin Oke-Ode a ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar akalla masu gadin daji goma sha daya da wasu mazauna yankin, tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Shugabannin tsaro sun ce za su ci gaba da farmakin har sai sun murkushe ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane gaba daya daga jihar Kwara da kewaye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here