A shirye nake na ja da baya idan matashi ya lashe zaben fidda gwani a jam’iyyar ADC – Atiku

Atiku Abubakar 750x430
Atiku Abubakar, Nigeria's main opposition presidential candidate, gestures during a Bloomberg Television interview in Lagos, Nigeria, on Wednesday, Jan. 16, 2018. Abubakar said he'll sell the state oil company, which he called a "mafia organization," and attract private investors to drive growth and create jobs if he wins office next month. Photographer: George Osodi/Bloomberg via Getty Images

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa a shirye yake ya ja da baya idan wani ɗan takara matashi ya kayar da shi a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2027 da ke tafe.

Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Laraba, inda ya ce yanzu yayi wuri ne a tabbatar da cewa zai tsaya takara, amma abin da yake fi mayar da hankali kai shi ne haɗa kan ‘yan adawa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Atiku ya kuma musanta jita-jitar cewa yana yin “takun-saka” tsakanin PDP da ADC, inda ya jaddada cewa ba a saba saninsa da yin hakan ba. Ya ce: “Idan na ce zan bi hanya guda, zan bi ta.”

A watan Yuli, Atiku mai shekaru 78 ya yi murabus daga Jam’iyyar PDP, inda ya ce jam’iyyar ta kau da kai daga tushen manufofinta na asali, don haka bai ga dacewar ci gaba da kasancewa cikinta ba.

Cikin wasikar da ya aike wa shugaban PDP na mazabar Jada 1 a jihar Adamawa a ranar 14 ga watan Yuli, Atiku ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar nan take.

Ya bayyana cewa wannan mataki ya zama dole saboda sabanin ra’ayoyi da ba za a iya sasanta su ba, lamarin da ya ce ya sa dole ya dauki wannan mataki mai nauyi.

Tun daga lokacin, Atiku ya dage wajen kafa tushe da tallafa wa jam’iyyar ADC, tare da jaddada cewa manufarsa ita ce ƙirƙirar hadin kan adawa domin kalubalantar gwamnatocin da ba sa tafiya da tsarin dimokuraɗiyya yadda ya kamata.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here