Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin binciken hukumar Hisbah kan zargin azaftarwa

Hukumar, Hisbah, Gwamnatin, Katsina, kwamitin, binciken, zargin, azaftarwa
Gwamnatin Katsina ta kafa kwamiti mai mutane bakwai da zai binciki zargin azabtar da mutane da jami'an hukumar Hisbah ta jihar ke yi. Wannan dai na zuwa ne...

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamiti mai mutane bakwai da zai binciki zargin azabtar da mutane da jami’an hukumar Hisbah ta jihar ke yi.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani faifan bidiyo da ake zargin jami’an hukumar na azabtar da mutane.

Sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Garba-Faskari ya ce matakin ya biyo bayan rahotanni da korafe-korafe da gwamnati ta samu.

Mukaddashin gwamnan jihar Faruk Lawal-Jobe ya bayar da umarnin a kafa kwamitin da zai binciki zargin tare da bayar da shawarwari.

Karin labari: Kotu ta yanke hukuncin rataya ga wasu mutane 3 kan laifin keta haddin matar aure a Kebbi

Garba-Faskari ya bayyana cewa kwamitin zai kasance karkashin kwamishinan matasa da wasanni Alhaji Aliyu Lawal.

Ya ce mambobin kwamitin sun fito ne daga ma’aikatun harkokin addini da tsaro na cikin gida da shari’a da kuma ma’aikatar kula da ayyukan gwamnati, tare da hadaddiyar kungiyoyin farar hula (CSOs), yayin da Daraktan Tsaro na ofishin SSG, zai zama sakatare.

An wajabtawa kwamitin binciken sahihancin gaskiya ko akasin haka na azabtar da wasu mutane da ake zargin jami’an Hisbah ne.

Ana sa ran kwamitin ya mika rahotonsa cikin kwanaki 10.

Karin labari: Hukumar DSS ta kama masu fataucin yara a Kano

Jihohi da dama a arewacin Najeriya ne suka kafa hukumar Hisbah bayan kaddamar da Shari’ar Musulunci a farkon shekarar 2000.

Hukumar Hisbah ta kunshi jami’an gwamnati da malaman addini da jami’an tsaro.

Tsarin aikin hukumar yana da ƙanƙanta sosai tare da ƙungiyoyin gida waɗanda kwamitocin da suka ƙunshi jami’ai da ‘yan ƙasa ke kula da su a yankunansu kamar yadda NAN ta wallafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here