Gwamnatin jihar Katsina, ta buƙaci da a soke jarabawar Turanci da hukumar shirya jarabawar yammacin Afirka WAEC ta gudanar a makon da muka yi bankwana da shi.
Gwamnatin ta yi wannan kira ne yau Asabar biyo bayan wani lamari ne da ya kai ga fara jarabawar sa’o’i da dama bayan wa’adin da aka sanya a fadin Najeriya a ranar Larabar da ta gabata.
Kwamishiniyar ilimin matakin farko da Sakandire Hajiya Zainab Musa-Musawa ce ta sanar da matsayin jihar ta Katsina yayin da ta kai ziyara ofishin WAEC da ke jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa gwamnatin ta miƙa roƙon soke jarrabawar ta cikin wata takarda da Hajiya Ummukhair Ahmed, babbar sakatariyar ma’aikatar Ilimi ta sanya wa hannu.
NAN ta kuma ruwaito cewa WAEC ta dora alhakin lamarin a kan yadda ake kokarin dakile taɓarɓarewa harkokin jarrabawa, musamman yadda aka rika fitar da takardun tambaya.
“Dalibai sun rubuta jarrabawar da dare ba tare da haske ba har sai an samar da haske ta yin amfani da fitilun wayar hannu,” in ji ta.
Musa-Musawa ta kuma yi kira ga makarantu da iyaye da sauran al’umma da su yi hakuri su jira sakamakon koken.
NAN













































