Gwamnatin Kano ta haramta gudanar da hawan daba da na dawaki

Kano Durban

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da hawan daba da na doki a cikin birnin Kano har sai an ji sanarwa ta gaba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada labaran Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature, ya fitar ranar Lahadi a Kano.

Ya ce an dauki matakin ne biyo bayan wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, inda aka yi nazari kan yanayin tsaro da ya shafi shirin hawan dawakin.

“Majalisar Tsaro ta Jihar ya yanke shawarar daukar matakan kariya don gujewa duk wata arangama, da kiyaye zaman lafiya da kauce wa duk wani yiwuwar asarar rayuka ko lalata dukiya.

“Gwamnati ta bayyana cewa rahotannin tsaro sun nuna cewa an yi wani gagarumin gangamin magoya baya dangane da wannan hawa da aka shirya, wanda ya haifar da damuwa game da yiwuwar arangama da tabarbarewar doka da oda.

“Bisa la’akari da alhakin da kundin tsarin mulki ya dora mata na kare rayuka da dukiyoyi da kuma kiyaye zaman lafiya da tsarin jama’a, Majalisar Tsaro ta Jihar ta ba da umarnin dakatar da shirin hawan daba da hawan doki,” in ji shi.

Bature ya ce majalisar ta umarci jami’an tsaro da su aiwatar da hanawar tare da daukar matakan doka da suka dace kan duk wanda ya karya doka.

Don haka ya bukaci mazauna, masarautun gargajiya, ‘yan siyasa, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da natsuwa, zaman lafiya, bin doka da kuma bin umarnin hanawar.

Ya kuma tabbatar da cewa ana daukar matakan da suka dace don kiyaye zaman lafiyar jama’a da kare rayuka da dukiyoyi a jihar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gudanar da hawan daba na musamman ranar Lahadi a Kano.

An fara gudanar da hawan dabar ne da misalin karfe 9:00 na safe daga gidan sarki na Nasarawa, kuma ta bi ta manyan tituna a cikin birnin.

Tawagar sarkin, tare da jami’an tsaro, ta bi ta titunan Jihar, Obasanjo da IBB, kuma ta wuce zuwa Kofar Wambai, Zage, Yola, Kwanar Gabari, ta kuma kare a gidansa da ke yankin Mandawari a cikin birnin Kano. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here