HOTUNA: Gwamnatin Kano ta fara raba murahun girki na zamani 3,400 ga mata masu karamin karfi

IMG 20260928 WA0099 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta fara raba murahun girki na zamani guda 3,400 daga Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ga mata masu karamin karfi a jihar.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir Hashim, wanda ya kaddamar da fara rabon a ranar Lahadi a Kano, ya ce shirin na da nufin rage hadarin lafiya da muhalli da ke tattare da amfani da itacen wuta wajen girki.

IMG 20260928 WA0104 768x512

SolaceBase ta ruwaito cewa WHO ta kiyasta cewa mutane miliyan 2.9 ne suka mutu sanadiyyar gurbacewar iska ta cikin gida a shekarar 2021, yayin da kimanin mutane biliyan 2.1 a duniya ke ci gaba da dogaro da gurbataccen man girki da fasahohi.

A Najeriya, samun damar girki mai tsabta ya yi kasa, inda mata da yara ke fuskantar hadarin lafiya musamman daga gurbacewar iska ta cikin gida.

IMG 20260928 WA0105

Hashim ya ce an riga an raba kimanin murahun girki na zamani guda 800 cikin nasara ga mata dake da karamin karfi a fadin jihar.

“Wadannan murahun girki na zamani wani bangare ne na muhahu 3,400 da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta ware wa Kano,” in ji shi.

IMG 20260928 WA0100 IMG 20260928 WA0103

Ya sanar da cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya kuma tallafa wa kowace daga cikin wadanda suka amfana 800 da Naira 25,000 don bunkasa kananan sana’o’insu da karfafa hanyoyin rayuwa.

A cewarsa, tallafin ya yi daidai da babban manufar gwamnati na rage hayaki zuwa mafi karanci da kuma inganta tsaftar hanyoyin da za a bi maimakon hanyoyin girki na gargajiya.

Kwamishinan ya bayyana cewa a tsawon shekaru, mata da yawa, sun jure matsanancin hadarin lafiya daga shakar hayaki mai guba da itacen wuta ke samarwa, saboda yawan amfani da hanyoyin girki na gargajiya.

IMG 20260928 WA0102 768x512

Ya ce shakar irin wannan hayaki na tsawon lokaci na iya haifar da mummunan hadarin ga lafiya, musamman matsalolin numfashi, inda ya bayyana shakarsa a matsayin daidai da shan taba sigari da yawa a kullum.

“Wadannan sabbin murahu za su rage wannan hadarin sosai kuma su kare su daga cututtukan numfashi,” in ji Hashim.

Ya bayyana cewa shirin girki na zamani wani bangare ne na kokarin da gwamnati ke yi na magance sauyin yanayi tare da inganta lafiya da yanayin rayuwar mata masu karamin karfi a jihar.

Hashim ya yaba wa Gwamnatin Tarayya saboda samar da murahun, ya kuma bukaci wadanda suka ci muriyar shirin da su yi amfani da abubuwan da aka ba su cikin hikima.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kuma himmatu wajen fadada shirye-shiryenta na tsaftar makamashi, ciki har da samar da hasken rana ga fitulun tituna da Ma’aikatu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here