Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta gayyaci al’ummai masu ra’ayin karin masarautu a fadin jihar da su mika takardar neman kafa sabbin masarautun da kuma gundumomi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Kwamared Mukhtar Gidado, wadda ya fitar ranar Litinin.
A yanzu haka dai jihar Bauchi na da masarautu guda shida ne wadanda suka hada da ta Bauchi da Katagum da Misau da Jama’are sai Ningi da kuma Dass.
Har ila yau, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a watan Disamban shekarar da muka yi ban kwana da ita ta 2024, ya amince da kafa masarautar Seyawa mai shalkwata a karamar hukumar Tafawa Balewa.
Muhammed ya bayyana cewa hakan na daya daga cikin kokarin gwamnatinsa na ganin an samar da dawwamammen zaman lafiya da mafita ga matsalolin da suka dabaibaye samar da masarautar Seyawa, wanda ya gurgunta kokarin gwamnatocin da suka shude sama da shekaru talatin.
SolaceBase ta ruwaito cewa lokacin mika takardun ya fara ne daga yau Talata 10 ga watan Yuni zuwa Talatar 8 ga watan Yuli, kuma za a gabatar da takardun ne a ofishin babban sakatare na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu Abubakar Umar da ke Sakatariyar Bauchi.













































