Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya nemi yan majalisar dokokin kano na jam’iyyar APC dasu taimaki gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf domin ciyar da jihar Kano gaba.
Abba Kabir, gwamnan kano a yanzu, wanda dan jam’iyyar hamayya ne, basa ga muciji da tsahon gwamnan kano wato Abdullahi Ganduje.
Gaduje ya nemi taimakon yan majalisu ne ya yin da suka kai masa ziyarar taya shi murna a ranar Litinin na samun shugabancin jam’iyyar APC na kasa.
Ya ce taimakon Abba Kabir Yusuf ba wai yana nufin sun juyawa jam’iyyar APC baya bane, sai dai kawai don ciyar da jihar Kano gaba.