A ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024, tawagar jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Enugu ta ziyarci Urban Radio 94.5FM, Enugu, domin gayyatar Favor Ekoh, dan amsa wasu tambayoyi.
Ana tuhumar Ekoh bisa zarginta da hannu a wani shirin Ponzi na Naira miliyan 700 wanda ya shafi kusan mutane 50 da abin ya shafa.
Wadanda abin ya shafa sun yi ikirarin cewa Ekoh ce ta sa su zuba jari a cikin shirin “Life Trading”, wani shiri da Leverage Index Limited ke gudanarwa, inda aka yi musu alkawarin samun kashi 10 cikin 100 na jarin su bayan wani wa’adi da aka kayyade.
Sai dai bayan sun zuba hannun jarin, kamfanin da ke No. 1 Colliery Street, Okpara Avenue, Enugu, ya rufe, inda ya bar su ba su da jarin su, ko kuma wani alkawari na dawowa.
Wadanda abin ya shafa sun ce Ekoh ce mutum ta farko da suka fara tuntuba game da shirin.
Da suka isa gidan rediyon tare da umarnin kama su, jami’an EFCC sun bayyana kansu ga Manajan Daraktan gidan rediyon, Bamikole Owoyomi.
Sai dai a wani mataki na ba zato ba tsammani, wani ma’aikacin gidan ya kira shugaban gidan rediyon, wanda ya ba da umarnin a kulle kofofin, inda ya makale jami’an EFCC a cikin ginin.
Daga nan ne jami’an suka nemi a ba su tallafi, lamarin da ya kai ga kama Owoyomi, Ekoh, da wasu jami’an tsaro guda biyu da suka kawo cikas ga ayyukan EFCC.
Ekoh, wacce aka bi ta gidan rediyon a wani mataki na hana ta kaucewa kama ta, an ba ta damar yin bayani a ofishin EFCC na Enugu, kuma tuni aka sake ta.
Owoyomi da masu gadin wadanda tun farko aka tsare su da laifin hana jami’an gudanar da ayyukansu, su ma sun yi bayani, daga bisani aka sake su.












































