Jigawa: Sama da mutum 90 ne suka mutu, 50 kuma suna kwance a asibiti sakamakon fashewar tankar mai – ‘Yan sanda

tanker fire

Wani mummunan lamari ya faru a daren ranar Talata, yayin da wata fashewar tankar mai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 90, yayin da wasu kimanin 50 ke kwance a asibiti, a Garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na rana a lokacin da motar tanka daga Kano ta nufi Nguru a jihar Yobe ta rasa iko a kusa da jami’ar Khadija, a karamar hukumar Taura.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu, ya ce duk da kokarin da ‘yan sandan suka yi na killace wurin tare da yin gargadi ga jama’a, amma jama’a sun yi turjiya tare da fara kwashe man, lamarin da ya haifar da mummunar fashewar.

Shiisu ya kara da cewa, ‘yan sanda sun yi ta kokarin ganin sun ci gaba da kula da wurin, inda jama’a da dama suka yi watsi da gargadin da aka yi musu, suka kuma yi tattaki kusa da wurin da hadarin ya faru.

“Motar mai dauke da man fetur, ta kone jim kadan bayan afkuwar hatsarin, wanda hakan ya janyo tashin gobara da ta kona mutane da dama a kusa da wajen.”

“Nan da nan aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ringim, inda jami’an kiwon lafiya ke aiki ba dare ba rana domin kula da wadanda abin ya shafa. Sai dai akwai yiyuwar adadin wadanda suka mutu ya karu saboda da dama daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

An tattaro cewa hukumomin yankin da malaman addini sun amince da gudanar da jana’izar jama’a ga wadanda aka kashe a safiyar yau, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here